some

AL-BASAR INTERNATIONAL FOUNDATION NIGERIA DA HADIN GUIWAR JIBWIS JIHAR BAUCHI BISA JAGORANCIN PROF. SHEIKH ZUBAIRU MADAKI SUN ƘADDAMAR DA SHIRIN GWAJE-GWAJE DA BADA MAGANI KYAUTA A SHIYYAR KATAGUM.

2 days ago Salim Yaya Azare

AL-BASAR INTERNATIONAL FOUNDATION NIGERIA DA HADIN GUIWAR JIBWIS JIHAR BAUCHI BISA JAGORANCIN PROF. SHEIKH ZUBAIRU MADAKI SUN ƘADDAMAR DA SHIRIN GWAJE-GWAJE DA BADA MAGANI KYAUTA A SHIYYAR KATAGUM.

An gudanar da aikin (Medical outreach) ne domin taimaka wa ƴan'uwa musamman masu fama da ciwon yanar ido. Kuma an gudanar da aikin ne a yau Alhamis 4/9/2025 a cikin masallacin Juma'a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake Kasuwar Kaji Azare. Kuma an dudduba mutanen da adadinsu ya kai mutane dari da casa'in da tara (199) daga kananan hukumomi 9: Katagum, Misau, Jama'are, Zaki, Gamawa, Shira, Itas/Gadau, Dambam da Giade, yayin da mutane talatin da takwas 38 daga cikinsu kuma za a kai su garin Bauchi Makka Eye Hospital don ayi musu aiki kyauta.
Shugaban ƙungiyar JIWBIS na jihar Bauchi Prof. Zubairu Abubakar Madaki yayi godiya wa gidauniyar Al-basar International Foundation bisa taimakon mutanen jihar Bauchi, kuma ya ƙara kira ga jama'a su cigaba da yin musu addu'o'i, da kuma samun nasara ga waɗanda za a yiwa aiki.

Salim Yahya Azare.