some

Yakamata mu fada wa juna gaskiya.

3 hours ago Salim Yaya Azare

Yakamata mu fada wa juna gaskiya.

Daga Sir-Kashim Ibrahim SK


A farkon tawayen da kake magana Usazu ai lokacin karatu bai yi yawa ba, kuma mutum nawa ne suka tafi jami'ar Madina suka yo digiri daga bangaren Jos a wancan lokacin?


Bayan baiyanar kungiyar Izalah ko kuma kafin baiyanar ta, an samu matasa sun fita zuwa neman ilmi wanda a baya babu masu karatu musamman ma masu fita Kasar waje.


Lokacin da aka samu baraka a kungiyar Izalah mafiya yawan daliban nan suna makaranta, lokacin da suka dawo Najeriya kungiyar ta rabe gida biyu, sai suka yi matsayar cewa ba zasu iya shiga dukkan wani bangare ba, kamar su Sheikh Jaafar Mahmud Adam(r) suka tsaya suka ci gaba da bude Majlisin su na karantarwa, amma mafiya yawan su suna alaka da bangaren izalar Kaduna ne, lura da su basu kyamaci kowa ba, sabanin bangaren mu inda muka karkata kurum wajen karantar da littatafan fiqhu a MAZHABAR MALIKIYYA kadai. Sai muke yi wa duk wanda yazo da wani ilmi ko karatu sabanin karantarwar MAZHABAR MALIKIYYA kallon wanda bai san komai ba ko wanda yake me kawo sabon abu a addini, kuma muka kyamace su, tabbas wadan nan dalibai idan sun dawo Najeriya muna samun sabani da su wajen musu kallon kamar sun zo da sabon abu ne wanda ya saɓa wa MAZHABAR MALIKIYYAR da muke kan ta, sam sam bamu yarda da su ba, wasu ma muka kore su daga masallatan mu, muka dena mu'amala da su, wannan kuwa bai rasa nasaba da cewa wasu daga cikin mabiya Sheikh Isma'ila Idris Ibn Zakariya wadan da suka makale a jikin sa basu yi wani karatu ba, kuma sune ke kokarin maye gurbin sa suka yi ta rura wutar gaba domin kada a samu wasu matasa wadan da idan sun zo ana tafiya da su za'a gane wadan nan fa ba ilmi suke da shi ba, Sheikh Isma'ila Idris da kansa bai dauke su a matsayin malamai ba da sunan su yake kiran su domin shi ya san ba malamai bane, amma wadan da mallam yasan malamai ne yana kiran su da sunan mallam wane, ba sai na ambace su duka ba, amma kadan daga cikin su akwai, mallam Adamu Ibrahim Me Shafi, Mallam Sa'idu Hassan Jingir, mallam Hassan Dikko, mallam Abbas Isah Lauya, mallam hamza Adamu Abdulhameed Gombe, mallam Abdurrahman isah Jega, mallam Aliyu Alhassan Sange, mallam Adamu Gasua, malaman suna da yawa sune kawai malamai a izalar Jos wadan da Sheikh Isma'ila Idris ya ke kiran su da sunan mallam domin yasan su malamai ne, akwai wadan da shuwagabanni ne ba malamai bane amma suna yiwa kungiyar hidima da sauran ayyukan.



Dan haka akwai wasu da suka yi ta rura wutar wannan gaba tsakanin bangarorin biyu saboda burin su na mallake kungiyar, wanda gashi nan a zahiri muna kallon abun da ke faruwa a halin yanzu, sun ki yarda a wancan lokacin su kyale matasan nan su shigo cikin mu, aka yi ta zargin su da zuwa da sabbin abubuwa a cikin ibada wanda bawai sabbi bane mu Kawai mun kebanta da mazhaba daya ce, amma su kuma sunje sunyi karatu a wani wuri da suke aiki da wata mazhaba dabam da tamu, dabam da wacca take mu, aka yi tayi musu wasu irin sunaye dabam dabam, aka ki a karbe su gudun kada su kasance sun baiyana ilmin su, wata rana su kwace wa wadan da suke ganin sune mataimakan Sheikh Isma'ila Idris, amma a zahiri ilmin su yayi karanci, shiyasa suka yi ta sukar wasu abubuwa da wadan can matasan malamai wadan da suka dawo karatu daga Madina KO wata kasa da shi, wanda a wancan mazhaba ba laifi bane amma mu mun takaita ne da mazhaba daya, wanda Ni har yanzu ina da fahimtar a rike mazhaba guda kada a cakuda mana yanayin ibadar da kuma shari'un mu a kotuna,saidai bana goyon bayan a kyamace su, ko a zagi abun da watakila ya tabbata daga Annabi Muhammadu(saw) wannan a takaice kenan. 


To amma bangaren Kaduna basu kyamace su ba suka kusance su suka basu dama shiyasa Kaga sun fi mu yawan malamai matasa harma da dattawa domin koda izala ta rabu mafiya yawan malamai suna bangaren Kaduna ne, dan haka suka fi yaduwa a nan gida Najeriya dama Afurka da da duniya baki daya, sune suka yada kungiyar Izalah a Afurka suna shiga wurare da yawa da sunana Izalah inda mu bama shiga su isar da sako, ba wata jahar da zaka je babu shugabancin su, ni shaida ne, domin nan kusa babu shugabancin mu a jahar Delta, Ni Sir-Kashim Ibrahim Sardauna na kawo ta yayin da su tuni sun mamaye ko ina a dukkan kudancin nan, saboda sun dauki matakin musulmi dan uwan musulmi ne, ba kungiyanci ba, suka baiwa matasa damar da mu bamu ba su ba, kuma mafiya yawan masu dawowa daga madina ko wata kasa tare da su suka fi kusanci, ana samun yan kadan masu bin tafiyar Jos cikin hak'uri, domin danne su ake yi a maida su ba komai ba saboda tsarin danniya da mulkin wadan da basu cancanta suyi shugabancin kungiyar raya ilmi da ilmantarwa ba.


Idan kuka lura koda taron karawa juna ilmi ake yi da muke yi a bangaren mu na Jos, zaka ga wanda ya bada takarda shekaru ashirin da suka gabata shine yau zai sake badawa a a yanzu, kenan yaci nashi lokaci kuma yazo yana cin na wasu, amma lura da yadda aka gabatar da laccar a dakin taro na JNI Kaduna, wanda matasa aka baiwa damar gabatar da takardun, karkashin jagorancin Ash-Sheikh Alhaji Abdullahi Bala Lau, wannan ta sanya suka yi nisa wajen ci gaban kungiyar Izalah domin sun ajiye abu ne a inda ya dace da shi. 



Mu kuma idan Kaga an baka dama to tabbas ka iya fadanci da yaba shugaban majalisar malamai da kambama shi da tara masa girma da nuna shi yafi kowa adalci ko iya shugabanci ko yafi kowa ilmi, to sai kaga an bashi dama yana hawa mimbari yana wa'azi, ko kuma de shi shugaban majalisar malamai sai ya yarda a dora ka a mimbarin kafin ka hau, ina tunawa yayin da muka je filin wa'azin Kaduna kafin ma shugaba shekh Bala Lau ya shigo fili da sauran shuwagabannin mun gabatar da kanmu, kuma aka dauki sunan Alaramma Rufai Gamawa Ibrahim da Alaramma Ustaz Mahdi Ya'u Sundu ba tare da ma shugaba ya sani ba, mai gabatarwa ya gabatar da daya daga cikin Alarammomin yayi karatu da babban malamin su, amma kunga yadda aka yiwa Alaramma Abdullahi Bappah Itass a Kebbi kowa yasan ba haka kawai bane, kawai dan yana tare ne da Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikun ne aka ki a dora shi a mimbari, wannan tafiya fa ita muke akan ta a tsawon shekaru tafiyar danniya da jahiltar da mabiya da wayo ga mutane, muna cikin duhu da kauyanci da kungiyanci da son zuciya, AlhamdulilLaahi yanzu mun gano akan kuskure muke shiyasa muka dawo daga waccar makauniyar biyaiya da da'ar yaudara ta son zuciya domin wanin ALLAH.


To kai dan matashi ka sani wannan karatu da kayi a kan hakan kawai zaka kare, kare kungiyanci da cewa wasu yan tawaye, dan kawai ka burge malamin ka, akan abin da ba bawai babu shi a addini ba, sai dai kace kawai MAZHABAR MALIKIYYA bata yarda da su ba kuma nima wasu daga cikin wasu abubuwa bana yin su, koda ina tare da izalar Jos badan ita nake sake hannu a sallah ba, badan ita nake sallama daya ba, badan ita nake wasu al'amura na addini ba, abun da yazo a littafi ne nake yi shiyasa zaka ga wasu da ba yan izalar tamu ba suma suna yin yadda muke yi, abun ba namu bane na musulunci ne.


Dan uwa Ustaz ka sake lale an wuce lokacin da zaka jefa wa mutane shakku a zukatan su da sunan TAWAYE ko DA'AR KARYA ko KUNGIYANCI ko SON ZUCIYA ko DAUKAR SHEHUN KU TAMKAR YADDA MUSHRIKAI SUKE DAUKAR SHEHUNNAN SU.


Yanzu ilmi yayi yawa duniya ta zama tamkar a tafin hannu take an waye an samu ci gaba, wadan nan abubuwan da kace wai tawaye ne silar zuwan su a Najeriya wannan iyaka jahilci ne da rashin wayewa da dibganci da kungiyanci kawai ke sanya ka fadi hakan.


Wannan a takaice kenan, daga dan uwan ku mai kishin Izalah me rukiyyar cire kungiyanci daga kwakwalen dibgaggu.


Sir-Kashim Ibrahim SK


O/C ANTI KUNGIYANCI


Jibwis Nigeria Nhq Jos


08136577848 WhatsApp.com
+2348071751380
Laraba
16/03/1447
10/09/2025