HUKUNCIN YIN HUƊUBA GA YARON DA AKA HAIFA Tambaya:
6 hours ago
Salim Yaya Azare
HUKUNCIN YIN HUƊUBA GA YARON DA AKA HAIFA
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Don Allah ina neman ƙarin bayani akan huɗubar suna da yadda ake yi.
Amsa:
Wa alaikum assalam. Kiran Sallah da iƙama a kunnen yaron da aka haifa bai inganta ba, saboda Hadisin kiran Sallah Tirmidhi ya rawaito shi da sanadi mai rauni, Baihaƙi ma ya rawaito shi a Shu'abul-imani, sai dai a sanadinsa akwai maruwaita guda biyu waɗanda ake tuhumar su da ƙarya. Hadisin da yazo akan yin iƙama kuwa, malamai sun ce Hadisi ne na ƙarya. Sai dai ya tabbata a Sunnah ana tauna dabino a sawa yaro a baki.
_Allah ne mafi sani._
_31-12-2013_
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa